1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kammala tattaunawar Geneva kan Siriya

February 15, 2014

An kammala zagaye na biyu na tattaunawa domin shawo kan rikicin kasar Siriya a birnin Geneva na kasar Switzerland ba tare da cimma nasara ba.

https://p.dw.com/p/1B9k8
Hoto: Reuters

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Larabawa dake shiga tsakani a rikicn Siriya Lakhdar Brahimi, ya nemi afuwar 'yan kasar Siriya sakamakon gaza cimma wani abun a zo a gani a taron Geneva da aka kammala tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan tawaye. Brahimi ya bayyana takaicinsa dangane da gaza cimma wata yarjejeniya a zagaye na biyu na tattaunawar inda ya ce ka wo yanzu ba a sanya wata sabuwar rana da za a yi zagaye na uku na tataunawar ba.

Ya ce a kwai bukatar duka bangarorin biyu su koma su yi tunani mai zurfi domin su dawo su zauna kan teburin shawara, inda ya kara da cewa sun dai amince da jadawalin taron amma a kwai bukatar su amince da yadda za a yi amfani da jadawalin, yana mai bayyana fatan komawa zagaye na uku na tattaunawar.

A hannu guda kuma 'yan adawar ta Siriya sun bayyana tattaunawar da mara amfani suna masu cewa tattaunawa ba tare da tabo batun kafa gwamnatin rikon kwarya ba bata lokaci ne kawai.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh