SiyasaJamus
Kamfanin Shell zai biya manoman Najeriya diyya
January 29, 2021Talla
Wata kotun daukaka kara ta kasar Holland ta umurci kamfanin mai na Shell da ya biya diyya ga wasu manoma a yankin Naija Delta da ke kudancin Najeriya, bayan samun kamfanin da laifin gurbata filayensu na noma.
Wata kungiyar fafutikar kare muhalli mai suna Friends of the Earth, ita ce ta taimaka wa manoman na Naija Delta wajen kalubalantar kamfanin a shekara ta 2008.
Kotun ta ce kamfanin na Shell ya biya diyyar ga wasu manoma hudu da suka shigar da karar.
Tuni kuwa kungiyar ta Friends of the Earth, ta yi marhabin da da wannan hukuncin da kotun ta yanke a yau Juma'a, tana mai cewa hakan nasara ce gagaruma ga kokarin kare muhalli da ma mutanen da ke rayuwa a kananan kasashe na duniya.