1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Kama masu safarar hauren giwa

Abdul-raheem Hassan
May 19, 2022

Hukumomi a Kudu maso Ggabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun kama tan daya da rabi na hauren giwa a cikin manyan motoci a birnin Lubumbashi.

https://p.dw.com/p/4BaEa
Elfenbein Simbabwe
Hoto: Tsvangirayi Mukwazh/picture alliance/AP

'Yan sanda sun kama mutane biyar amma biyu sun gudu bayan an yi musu tambayoyi, kamar yadda lauyan kungiyar hadin guiwar kungiyoyin kare muhalli Sabin Mande ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP. A cewarsa, ya ga buhunan hauren giwar 18 da aka kama a ofishin mai shigar da kara na jihar da ke Lubumbashi.

Ana zargin masu safarar hauren giwar sun yanka adadin giwaye akalla 80 zuwa 100, sai dai haryanzu ba a tabbatar da inda aka fito da hauren giwar ba ko inda aka nufa da shi. Wannan dai shi ne kame mafi girma a Afirka cikin shekarun baya-bayan nan, bayan da Kenya da Togo suka kama ton hudu na hauren giwar a shekarun 2013 da 2014.

Kasar Sin da Kudu maso Gabashin Asiya dai sune manyan kasuwannin hauren giwar na Afirka, wanda akasari ake amfani da su wajen yin maganin da ake zargin na gargajiya ne.