SiyasaAfirka
AFCON: Kamaru ta yi raga-raga da Burkina Faso
January 9, 2022Talla
Kasar Kamaru mai masaukin baki a gasar cin kofin Afirka ta AFCON da aka bude a yammacin wannan Lahadi ta fara gasar da kafar dama. A fafatawar da suka yi tsakaninsu da Burkina Faso, Kamarun ta yi nasarar zura kwalla 2 a raga, a yayin da Burkina Faso ta yi kokarin zura wa kamaru kwallo guda 1.
Tun da farko sai da aka dauki lokaci ana bikin bude gasar da ke zama mafi daukaka a harkar kwallon kafa a nahiyar Afirka kafin a amincewa kasashen biyu da ke a rukunin A su kece raini.
An jima kadan da misalin karfe 8pm agogon Najeriya kasar Cape Verde da Habasha da su ma ke cikin rukunin A za su barje gumi a tsakaninsu a wannan gasa ta AFCON.