1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Shugaba Paul Biya ya gaza a Kamaru?

Fotso Henri MT/LMJ
May 8, 2019

A kasar Kamaru wani sabon kudirin shugaban kasar na bai wa magatakardar fadar gwamnati Ferdinand Ngoh Ngoh damar saka hannu a takardu a madadin Shugaba Paul Biya ya janyo muhawarar masana dokoki da ma al'ummar Kamarun.

https://p.dw.com/p/3IBNw
Kamerun Wahl l Präsident Paul Biya
Shugaba Paul Biya na KamaruHoto: picture alliance/dpa/j. Warnand

Da dama dai na ganin gajiwar Shugaba Biya ce mai shekaru 85 a duniya, wanda kuma ya shafe shekaru 37 a kan karagar mulkin kasar ta janyo wannan sabon tsarin. Tun ranar biyar ga watan Fabarairun wannan shekara ta 2019 ne dai Shugaba Paul Biya ya dauki kudurin mai bai wa magatakardar fadar tasa Ferdinand Ngoh Ngoh cikakkiyar damar  zartarwa a madadin shugaban kasar, musamman ma saka hannu a takardu. Sai dai bayan shafe watanni uku da aiwatar da wannan kudirin, muhawara ta kaure a tsakanin masana doka da 'yan siyasar kasar, lamarin da ya kai da dama tambayar shin ko dokokin kasar sun tanadi yin hakan? Maitre Fidele Djoumbissie lauya a mashar'antar Kamaru kuma dan jam'iyar adawa ta MRC na ganin cewa kudirin ba shi da tushe bare makama, inda ya ce:

 ''Kundin tsarin mulki ayar doka mai lamba 10 ta shata cewa shugaban kasa na iya danka wasu daga cikin nauyin gudanarwa ga firaminista ko sauran ministoci ko wasu ma'aikantan hukomin koli na kasa, amma maganar saka hannu a takardu a madadin shugaban kasa babu inda kundin tsarin mulkin ya yi wannan batu''

Sai dai magoya bayan gwamnatin ta Paul Biya, na ganin halaccin yin hakan kuma a cewar Ayissi Bessala memba a jam'iyar RPDC wannan kusan shi ne karo na hudu da Shugaba Biya mai shekaru 85 ke bayar da irin wannan dama ga wani magatakardan fadarsa. To sai a ta bakin Maitre Djoumbissie al'ummar kasar na iya yi wa shugaba Biya uziri, idan da ya bayar da kwakkwarar hujjar da ta sanya shi gabatar da wannan kudirin, misali ko yana cikin halin gajiwa ne ko kuma na tafiya, amma a hakan akwai lauje cikin nadi.