1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kamaru: Kalubalen yan jarida da matakin gwamnati

Zakari Sadou
August 13, 2024

Hukumar da ke kula da 'yan jarida a kasar Kamaru ta dauki matakin dakatar da wasu kafofin yada labarai guda shida da yan jarida masu gabatar da shirye-shirye sakamakon yada kalamain kiyayya kan gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/4jOcT
Kenia Pressefreiheit | Demonstration gegen ein Mediengesetzt in Nairobi
Hoto: Xinhua/IMAGO

Hukumar da ke kula da kafofin yada labarai ta kasar Kamaru, Conseil National de la Communication (CNC) a takaice, ta dakatar da wasu kafofin yada labarai da wasu yan jaridun da ke gabatar da shirye-shirye na tsawon wata guda zuwa watanni shida kan yada kalaman kiyayya kan gwamnatin kasar a cikin shirye-shiryensu.

Joseph Chebongkeng shugaban hukumar ya sanar da hakan a wata zama da hukumar ta yi a karshen makon da ya gabata.

Hukumar ta ce gidan rediyon RIS an dakatar da sbhi na tsawon watanni shida da darakatansa kan wasu kalamai na cin mutunci da aka yi wa wasu a lokacin wani shirii na gidan rediyo da talabijin na Équinoxe da ake gabatarwa kowacce ranar lahadi tare da mai gabatarwa na tsawon wata guda.

'yancin fadin albarkacin baki na 'yan Jarida a Afirka
'yancin fadin albarkacin baki na 'yan Jarida a AfirkaHoto: Isaac Kaledzi/DW

Dakatarwar ko gargadi da hukumar kula da yada labaran ta yi,ya tada hankalin kungiyoyin farar hula da yan jarida a kasar inda suka yi Allah wadai da matakan da mahukuntan Kamaru ke dauke domin tauye hakkinsu.

Lindovi Ndjio dan jarida Nouvelle Expression wanda ya kwashe sa'o'i 48 yana tsare ba tare sanin abin da yayi ba an tsare shi ne sakamakon zanga-zangar da yan adawa suka gudanar a shekarar 2019 inda suka kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar 2018

Ga dan jarida Wada Alhaji, kalubalen da yan jarida ke fuskanta a wannan kasa shine rashin basu damar gudanar da bincike kan ma'aikatan gwamnati domin kawo haske kan ayyukan da suke yi wa kasa

Taron 'yan Jarida na duniya
Taron 'yan Jarida na duniyaHoto: Marwan Tahtah/Samir Kassir Foundatio

'A nan kasar Kamaru zamu iya ce gwamnati na da cikakken iko kan kafofin yada labarai dalilin haka ne ma ta kafa CNC wato hukumar kula da kafofin yada labarai to ka ga dai yayin da yan jarida suka bankado wani labari ko kuma suka yi wani shiri a gidajen talabijin ko rediyo idan dai gwamnati ba ta gamsu da wannan ba za ka ga an dakatar da wannan kafar ko yan jaridar da suka tafiyar da wannan mahawara to ka ga ba za a ce akwai cikakken yanci a nan kasar Kamaru wajenn fadin albarkacin baki ga dan jarida ba''

 Philipp Nanga shugaban kungiyar farar hula la Monde Avenir ya ce ya kasa gane gazawar gwamnati wajen bincike domin gano wadanda suke da hannu kan kisan gillar da aka yi wa dan jaridar nan Martinez Zogo yau sama da shekara guda

 ‘'Mun ga yadda wasu ministoci suke yi wa yan jarida barazana bayan haka aka tsare wasu kuma aka samu asarar rayuka.''

Kamaru ta koma kasa a teburin kasashen da ke mutunta yancin yan jarida, ta tashi daga lamba 138 a 2023 ta koma ta 130 inji rahoton da kungiyar kare hakkin yan jarida ta kasa da kasa ta fitar a wannan shekarar.