1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya barke a yankin Bamenda

Binta Aliyu Zurmi
October 1, 2019

Rahotanni daga Bamenda da ke kasar Kamaru na nuni da cewa 'yan aware masu rajin ballewa daga kasar yanzu haka na can suna dauki ba dadi da jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/3QZrI
Kamerun Sprachenstreit Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Wannan na zuwa ne rana guda bayan da gwamnatin kasar ta fara wani zaman sulhu da su yan awaren da nufin sasanta matsalar da ke tsakaninsu. Amma bangaren yan awaren sun ki su halarci wannan zaman, kuma sun hana mutane fitowa daga gidajen su. 

A yau daya ga wata Oktoba ne yan awaren ke ikirarni ranar da Ambazoniya ta sami yancin kanta wanda su ka ce sai sun daga tutar su. Haka zalika yau ake cika shekaru biyu cir da ballewar rikici a kasar.