1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Armeniya da Azarbaijan na zafi

Ehli David SB/LMJ
October 7, 2020

Dakarun Armeniya da na Azarbaijan sun kwashe fiye da mako guda suna musayen wuta. Amma akwai kasashe dabam-dabam da ke tsoma baki a cikin rikicin.

https://p.dw.com/p/3jaMN
Berg-Karabach Konflikt
Rikicin Armeniya da Azarbaijan na lakunme rayukaHoto: Aram Kirakosyan/PAN Photo via AP/picture-alliance

Rikicin tsakanin Armeniya da Azarbaijan ya janyo mutuwar daruruwan sojoji da fararen hula daga duk bangarorin biyu. Stefan Meister ke shugabancin ofishin gidauniyar Heinrich Böll ta Jamus a birnin Tbilisi fadar gwamnatin Jojiya mai makwabtaka da yake ganin lamarin ya zama karfe kafa: "Abin da nake ji shi ne mutane da yawa sun halaka daga dukkan bangarorin biyu. Yanayin ya tsananta, ba abu ne mai sauki ba wani daga waje ya sasanta rikicin a kwana daya. Yaya za a kawo karshen rikicin da wuri? Wannan shi ne abin da muke dubawa."

Tsohon miki ne ya tashi?

Wannan rikicin kan yankin Nagorno-Karabakh ya fara kunno kai tun bayan rushewar tsohuwar Tarayyar Soviet, inda kasashen suka fara kai ruwa rana tun farkon shekarun 1990. Tun a wancan lokacin ake samun barkewar rikici lokaci zuwa lokaci. Yankin Nagorno-Karabakh yana karkashin ikon Azarbaijan, wanda ya ayyana samun gashin kai a shekarar 1991. Sai dai babu wata kasa a duniya da ta amince da haka. Galibi Armeniyawa ne ke rayuwa a yankin na Nagorno-Karabakh, wanda ya saka Armeniya dagewa cewa yankin ya zabi makomarsa.

Deutschland Stefan Meister
Shugaban ofishin gidauniyar Heinrich Böll ta Jamus a kasar Jojiya Stefan Meister Hoto: DGAP/D. Enters

Stefan Meister na ganin Rasha tana baki biyu game da rikicin: "A tunaninsu, tana taka rawa domin daidaita karfi tsakanin kasashen, amma ba mai kare Armeniya ba ce. gaskiya Armeniya ba ta jin tana karkashin wata kariya daga Rasha, sai dai tana tunanin Rasha tana taka rawa biyu. Muna ganin yadda Rasha ta mayar da martanin da babu karfi yayin da Turkiya take kara nuna karfi, ba ga goyon bayan Azerbaijan kadai ba, har ma dda shiga ta fannin soja a bangaren Azerbaijan."

Tarayyar Turai ta yi watsi da rikicin

Sannan Stefan Meister ya kara da cewa kungiyar Tarayyar Turai ta mayar da hankali kan wasu rikice-rikice da ke kusa da ita, fiye da rikicin kasashen kasashen na  Armeniya da Azerbaijan: "Yankin Caucasus ya kasance wanda ya yi nisa, abin da ya sa mahukuntan Turai da ke birnin Brussels suke mayar da hankali. Akwai wasu rikice-rikice yanzu haka kamar na Belarus, ga rikicin madugun 'yan adawa na Rasha, wadannan sun fi jan hankali."

Jamus wadda ke rike da shugbancin karba-karba na kungiyar Tarayyar Turai, tana taka rawa domin ganin kungiyar ta samar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin kasashe Armeniya da Azarbaijan da ke dauki ba dadi.