1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Kamala Harris na samun goyon bayan 'yan Democrat

July 22, 2024

Kamala Harris ta shiga takarar neman shugabancin Amurka ne bayan shugaba Joe Biden na jam'iyarta ta Democrat ya goya mata baya.

https://p.dw.com/p/4iZbA
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala HarrisHoto: picture alliance/NDZ/STAR MAX/IPx

Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris na ci gaba da samun goyon bayan tsayawa takara daga shugabanni da 'ya'yan jam'iyyarta ta Democrat. Jam'iyyar za ta gudanar da babban taronta a watan Agusta domin fitar da mai fafatawa da Donald Trump na Republican a babban zaben Amurka na watan Nuwamban 2024. Kamala ta nemi hadin kan sauran 'ya'yan jam'iyyar  bayan samun goyon bayan shugaba Biden da ya fice daga takarar saboda damuwa da aka rika nunawa kan tsufa da kuma lafiyarsa.

Karin bayani: Shugaba Joe Biden ya janye daga takara

Majiyoyi da dama sun bayyana an fara kiraye-kirayen da zummar toshe kofa ga duk wanda ke son shiga takara da Haris. Har ila yau, an bayyana cewa shugabannin jam'iyyar Democrats a jihohin Amurka da dama sun nuna goyon bayansu ga mataimakiyar shugaban na Amurka Kamala Harris.

Ana sa ran ficewa daga takarar shugabancin Amurka da Joe Biden ya yi ta mamaye taron da ministocin harkokin waje na Tarayyar Turai za su yi a ranar Litinin a yayin da ake nuna damuwa kan yiwuwar lashe zabe daga bangaren Donald Trump a karo na biyu. Muhimman batutuwa da aka tsara tattaunawa tunda farko sun hada da rikice-rikicen Ukraine da na Gabas ta Tsakiya, amma wannan matakin na Biden zai iya samun fifiko a taron da zai gudana a Brussels.

Karin bayani: Donald Trump na kan hanyarsa ta zama shugaba

Shawarar da Biden ya yanke ta hakura da tsayawa takara ta jefa jam'iyyarsa ta Democrats cikin tunanin wanda zai fi cancanta ya fuskanci Donald Trump na Republican a zaben biyar ga watan Nuwamban 2024. An yi ta zaman doya da manja tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Amurka  a wa'adin farko na Trump a matsayin shugaban kasa. Ko da yake ba dukkan kasashen Tarayyar ne suka nuna damuwa kan batun ba.