1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaBurundi

Burundi: Kalubalen karatun firamare

October 1, 2024

A shekara ta 2013 gwamnatin kasar Burundi ta aiwatar da sauye-sauye da suka kara adadin shekarun da yara za su kwashe a makarantun firamare da shekaru uku, inda a yanzu suke shafe shekaru tara maimakon shida.

https://p.dw.com/p/4lIVM
Burundi | Yara | Makarantu | Firamare
KAlubale sababbin tsare-tsaren makarantun Firamare a BurundiHoto: picture alliance/dpa-Zentralbild/T. Schulze

Gwamnatin ta Burundi ta dauki wannan matakin ne, domin tabbatar da yara sun samu karatu mai inganci ko da ba su samu damar ci gaba ba duk da cewa sabon tsarin na haifar da matsaloli. Bayan shafe tsawon shekaru 11 ana aiki da sauye-sauyen da gwamnatin kasar ta Burundi ta kaddamar na shekaru tara a makarantun firamaren maimakon shida, matakin ya kara yawan kudin da gwamnatin ke kashewa gami da yawan lokacin da iyalai suke yi wajen taimakon yaran da suke kananan makarantun. A shekara ta 2016 shekaru uku bayan kaddamar da sauye-sauyen tsarin ilimin kasar ta Burundi, aka fara jarabawar kasa tsakanin wadanda suka shekara tara a makarantun firamaren kasar. A lokacin kimanin kaso 70 cikin 100 na dalibai sun samu kyakkyawan sakamako, a wannan shekara kuma aka samu kaso 80 cikin 100 na daliban da suka samu nasara a jarrabawar. Sai dai wannan kari na nasarar da aka samu ya faru ne sakamakon rage yawan makin da ake bukata kafin dalibai su samu nasara, inda a shekara ta 2017 aka mayar da shi zuwa maki 85 cikin 200.

Burundi | Yara | Makarantu | Firamare
Kokarin inganta ilimin firamare a BurundiHoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Wani dalilin shi ne, ana samun yaran da ba sa kammala makarantun firamare din. Adadin daliban da ba su kammala makarantunsu na firamare ba ya tashi daga kaso 10 da doriya cikin 100 zuwa kaso 15 cikin 100 tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2016, kamar yadda Hukumar Tsare-tsaren Makarantun Firamare ta Burundin ta tabbatar. Victor Ndabaniwe yana cikin 'yan kungiyar kwadago, wanda ya yi imanin cewa ana bukatar sake duba sauye-sauyen da gwamnatin ta aiwatar ganin yadda harshen Faransanci ya yi kasa. Albashin malaman makaranta a kasar ta Burundi bai taka kara ya karya ba, kana babu isassun kayan aiki. Azuzuwa sun cika sun tumbatsa, inda ake samun fiye da yara 50 da ya kamata a samu a ka'ida a kowane aji. Sannan ana kara samun makarantu masu zaman kansu, duk wadannan na nuna da irin bukatar da ake da ita na sababbin sauye-sauye a makarantun kasar.