1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta tsaida Tesla wajen kafa kamfaninta na farko a Jamus

December 10, 2020

Masu kare muhalli a Jamus sun samu nasarar karar da suka maka kamfanin motoci na Tesla a wata kotun Birlin.

https://p.dw.com/p/3mXwe
Deutschland Grünheide | Baustelle Tesla
Hoto: Patrick Pleul/AP Photo/picture alliance

Yunkurin kamfanin motoci na Tesla na kafa wani katafaren kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki a nahiyar Turai ya gamu da tsaiko, bayan da wata kotu a Birnin Berlin ta dakatar da shi daga sare itatauwa a wurin da ake tsammanin kafa kamfanin.

Wasu kungiyoyin masu kare muhallin ne suka shigar da kamfanin kotu, inda su ke zargin kamfanin da fara aiki ba tare da an sauyawa dabbobin da ke dajin matsugunnai ba.

Kungiyoyin dai sun sami nasara a kotun, bayan da su ka ki amincewa da hukuncin da wata karamar kotu ta yi tun da fari.