Sana'ar lemon mara sinadari
April 17, 2019Kabiru Sani ya ce ya rungumi wannan sana'a domin ya riba ci zamani. Tatsar ruwan lemu ba wani sabon abu bane a biranen Najeriya, domin akwai kananan injuna da ake kira blenders da magidanta kan yi irin wannan jus din a gidaje.
Sai dai ba a cika samun jama'an da kan rungumi irin wannan a matsayin sana'a ba. Kabiru ya ce ba jus din lemu kadai suke samarwa ba. Samar da lemon kwalba wanda babu wani sinadari a cikinsa abu ne da ke samun karbuwa musamman ga jama'an da ke taka-tsamtsan a irin abincin da su ke kaiwa bakinsu.
Cinikin da jama'a irinsu ke yi wa Kabiru tuni ya ba shi damar samar wa matasa guda goma sha biyar aikin yi a wurin kasuwancinsa. Kuma bayan samar wa wadannan matasa tundun dafawa, ya ce a cikin shekaru takwas da ya kwashe yana wanann sana'a, Izuwa yanzu ya ga alfanun dogaro da kai.