1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mai kera tukwanen gargajiya a Kaduna

March 21, 2019

Wani Matashin Kaduna da ya kammala karatu ya yi watsi da aikin gwamnati da kampani, inda ya kirkiri na shi sana’ar ta kera tukwanen gargajiya zuwa na zamani tinda ya ke amfani da dalma

https://p.dw.com/p/3FS1E
Bangladesch Töpferei
Hoto: DW/M. Mostafigur Rahman

Matashin yana kuma kera wasu sabbin Tukwanen-Tandar-waina, da Murhu toya kosai na zamani ta hanyar narka tsaffin karafuna da ruwan Dalma dan  rufawa kansa asiri.

Kasuwar fanteka a kaduna, kasuwa ce da matasa masu yawan gaske da suka kammala karatu, da ma wadanda ke ci-gaba da karatunsu kama sana'ar kere-keren zamani don rufawa kansu asiri.

Saleh umar na daga cikin matasan da suka yi watsi da aikin gwamnati, ya rungumi sana'ar kera sabbin tukwanen zamani da tandar waina da murhun toya kosai da sauren tukwanen girke-girken abinci na zamani da ruwan dalma da suke anfani da tsoffin tarkacen karafan mota da suke cire alminiyom dan sarrafa shi zuwa abubuwa daban daban da suke bukata.

A cewarsa dai akwai nasarori masu dumbum yawa da ya samu tun lokacin da ya kama wannan sana'ar:

Daga cikin nasarorin da ya samu sun hada na bunkasar harkokin kasuwanci na da kuma samun iyali da horar da matasa masu yawar gaske, kuma a kowace karshen shekara suna samun damar yaye wadanda suka kammala daukar horo dan su su zamo masu cin gashin kansu.

Saleh ya nunar da cewa Akwai kalubale duk kowa da cewa yana samun kwanciyar hankali da wannan sana'ar ya ce babban kalubalen mu shi ne dai na karancin tallafi daga bangaren hukumomi dan bunkasa wannan sana'a, sannan kuma akwai bukatar samun goyan baya daga  bangaren iyayen yara wajen kara masu kwarin guiwa domin zuwa daukar horo.