1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaddamar da leken asiri ta sararin samaniya

Abdullahi Tanko Bala
May 30, 2023

Koriya ta Arewa za ta kaddamar da naurarta ta farko ta tauraron dan Adam don binciken ayyukan soji na leken asiri ta sararin samaniya kamawa domin bin diddigin motsin daga Amurka da Koriya ta Kudu

https://p.dw.com/p/4RykY
Hoto: Ahn Young-joon/AP Photo/picture alliance

Mataimakin shugaban hukumar lura da al'amuran soji na Koriya ta Arewa Ri Pyong Chol ya ce ana bukatar naurar tauraron dan Adam  din a sararin samaniya domin dakile abin da ya kira atisayen soji mara ma'ana da Amirkar ke yi da Koriya ta Kudu.

Sanarwar na zuwa ne kwana guda bayan da Koriya ta arewa ta sanar da sojojin Japan masu tsaron gabar ruwa game da manufar da ta ce za ta aiwatar tsakanin 31 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Juni. Tana mai cewa kaddamar da kumbon tauraron dan Adam din zai shafi kogin gabashin China da tsibirin Luzon a gabashin Philippines

Yayin da kasashen yamma suka soki yunkurin Koriya ta arewa na kaddamar da tauraron, babu tabbas ko karfin tauraron ya kai yadda zai iya lura da ayyukan sojin Amurka da Koriya ta kudu.