1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kacici-kacici Ranar ‘Yancin Dan Adam

Mohammad Nasiru Awal
December 9, 2020

Kun san yaushe aka kaddamar da Kudurin Hakkin Dan Adam? Shiga cikin gasarmu ta Ranar ‘Yancin Dan Adam ka ci kyauta!

https://p.dw.com/p/3mIIy
Aayar hannu ta Huawei da abubuwan da ke zuwa da ita kamar ma'ansar kunne da amsa kuwa da madubai da sandar selfie da pop socket da kuma adaptar tafi da gidanka
Kyauta: Wayar hannu ta Huawei da abubuwan da ke zuwa da ita Hoto: Jeanette Fuchs/DW

Albarkacin Ranar ‘Yancin Dan Adam ta bana (10.12), DW Hausa ta kaddamar da gasar kacici-kacici da za ta gwada saninku kan muhimmancin ranar gareku, tarihinta da kuma ainihin rawar da ‘Yancin Dan Adam ke ci gaba da takawa a wannan duniya tamu, musamman a sassan da aka fi yi wa dan Adam barazana.

An kirkiro ‘Yancin Dan Adam ne don karfafa ‘yancin walwala ga mutane a duniya baki daya, ba tare da la'akari da yanki ba, a kuma kare su daga cin zarafi da kuma illa ga rayuwarsu.

Ku amsa tambayar da ke kasa don fahimtar saninku game da batun ‘Yancin Dan Adam. Za ku iya cin kyautar babbar wayar hannu ta Huawei da abubuwan da ke zuwa da ita kamar ma'ansar kunne da amsa kuwa da madubai da sandar selfie da pop socket da kuma adaptar tafi da gidanka!