Juya baya ga Trump kan Tuddan Golan
March 27, 2019Al'ummomin kasa da kasa sun yi rubdugu kan Shugaba Donald Trump na Amirka bayan da a ranar Litinin ya rattaba hannu kan amincewa da yankin Tuddan Golan da ake takkadama a kansa ya zamo mallakar Isra'ila. Martanin kasashen da ke fita a ranar Talata daga sassa dabam-dabam na duniya ya nunar da hadewar masu adawa da manufofin Amirka wuri guda.
A birnin New York mambobi daga kasashen Turai zuwa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kama daga Beljiyam da Faransa da Jamus da Poland sun yi fatali da matsayar ta Amirka inda suka ce ba su amince da cewar Isra'ila ke da mallaki na yankin Tuddan Golan ba.
A cewar hadakar mambobin kasashen, mamayar wani yanki ga wata kasa ta karfi ya saba wa dokar kasa da kasa, haka nan samar da kwaskwarima ga iyakar kasa ta irin wannan hanya.