1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya kori majalisar gudanarwa ta NNPC

July 17, 2012

A wani sabon yunkuri na gyara harkokin kamfanin kula da albarkatun man fetir na NNPC gwamnatin kasar ta sallami majalisar gudanarwar kamfanin amma banda ministan man fetur

https://p.dw.com/p/15ZCf
Hoto: picture-alliance/dpa

Ci gaba da tankade da rairaiyar da ake hangen gwamnatin Najeriyar na yi a kamfanin  kula da albarakatun man fetir din kasar, da ke zama wani yunkuri na tsarkake sashin da ya yi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa a kasar, musamman ma dai binciken baya baya nan da kwamitin majalisar wakilan Najeriyar ya gudanar a kan yadda aka yi wandaka da dukiyar kasar da ta kai fiye da trilliyan guda da sunan tallafin mai ga talakawan da suka tabbatar da basu gani a kasa ba.

Duk da cewa gwamnatin ta rusa majalisar  gudanarwa kamfanin man na NNPC tare da nada sabuwa, abinda ke nuna kokarin yin sabuwar shimfida ga sashin, don maido da martabarsa, to sai dai kawar da kai da gwamnatin ke ci gaba da yi ga wasu tisararu a mai'aikatar, da suka hada da ministan man Najeriyar da ta  kasance jagora a lokacin da kwamitin majalisar wakilan Najeriya ya yi wannan zargi, na sanya daga yar yatsa da tambayar illar da wannan ke da shi ga ikirarain da gwamnatin Najeriyar ke yin a yaki da cin hanci da rashawa a wanan sashi. Malam Sani Adbullahi shine daraktan cibiyar kare hakoki da ma yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya.

Sashin man fetir din Najeriyar dai ya dade yana fuskantar zargin cin hanci da rashawa a cikin kasar  musamman kasancewarsa babbar hanyara da kasar ke samun kudin shigarta, wannan ya sanya  shi kasancewa sashin da ke daukan idon alummar kasar da ke kasancewa mai cike da sarkaiyar gaske.

Wannan ya sanya ci gaba da yunkuri mayar da daukacin harkar a hannun yan kasuwa abinda ke fuskantar cikas, to sai dai ga Hon Ahmad Babba Kaita na kwamitin kula da harkokin main a mai ra'ayin cewa gina lamarin bisa gaskiya ne sahihiyar mafita.

Goodluck Jonathan
Shugaban Taraiyar Najeriya Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

Batun rashin hukunta wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa a Najeriya na zama babban kalubale da ke kawo cikas a duk yunkurin da shugabanin kasar ke ikirarin yin a samar da sauyi mai ma'ana a muhimman sassan kasar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu