1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

John Kerry ya shiga cikin tattaunawar shirin nukiliyar Iran

Mohammad Nasiru AwalNovember 20, 2014

Yanzu haka dai an shiga zagaye na karshe na tattaunawa game da shirin nukiliyar Iran da ake takaddama kai.

https://p.dw.com/p/1DqUQ
Atomgespräche Iran 11.11.2014
Hoto: Getty Images

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry yana kan hanyar zuwa birnin Vienna domin shiga cikin tattaunawar nan mai wahalar gaske game da shirin nukiliyar kasar Iran. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce Kerry na son ya shaida yadda tattaunawar ke tafiya. Kerry wanda ya yada zango a birnin Paris na kasar Faransa, yana tattaunawa da ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius. Yanzu haka dai an shiga zagaye na karshe na tattaunawa game da shirin nukiliyar Iran da ake takaddama kai. A ranar 24 ga watan nan na Nuwamba wa'adin da aka amince tsakanin Teheran da kasashe biyar masu kujerun dindindin a Majalisar Dinkin Duniya hade da kasar Jamus game da cimma wata dauwamammiyar yarjejeniya, zai kare.