1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin saman jigila kirar China ya fara aiki

May 28, 2023

China ta kaddamar da jirgin saman jigilar fasinja na farko da kasar ta kera da nufin yin gogayya da kasashe Yamma a fanni sufirin jiragen sama.

https://p.dw.com/p/4RuNS
Hoto: AFP via Getty Images

Jirgin saman sanfarin C919 mallakar kamfanin China Eastern Airlines dauke da fasinjoji 130 ya tashi daga filin sauka da tashi jiragen sama na birnin Shanghai domin isa Pekin babban birnin kasar.

Hukumomin Bejin na karfafa fatan wannan jirgin sama wanda kanfanin kere-kere na Comac ya samar zai yi hamayya da jiragen zamani da duniya ke alfahari da su irinsu Boeing da kuma Airbus.

Daga wannan Litinin mai zuwa jiragen kirar China sanfarin C919 wadanda aka inganta da kimiyar karshe za su fara zirga-zirga gadan-gadan a fadin kasar.

Tuni dai wasu kasashe suka fara nuna kadaiyinsu na cefano jiragen kirar Chaina, kuma a cewar mataimakin shugaban kamfanin na Comac wanda ke kera su kawo yanzu sun sami akalla oda ta jirage 1.200.