1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An bude zirga-zirgar tsakanin Saudiyya da Katar

January 11, 2021

Jirgin fasinja ya sauka a Saudiyya a wannan Litinin bayan ya taso daga kasar Katar. Wannan shi ne karo na farko a cikin shekarun uku da aka yi irin wannan zirga-zirga a tsakanin kasashen da ke a yankin Gulf. 

https://p.dw.com/p/3nnUz
Katar Doha - Qatar Airline Landet
Hoto: Getty Images/AFP/K. Jaafar

Bayan jigilar fasinjar da jirgin kamfanin Qatar Airways ya yi ta sa'a daya zuwa Saudiyyar, ita ma Saudiyya din ta shirya tashin wani jirgin fasinja a wannan Litinin zuwa kasar Kasar din. 


Kasashen biyu na yunkurin sasanta zaman doya da manjar da suka fara a shekara ta 2017, lokacin da Saudiyya ta zargi Katar da daukar nauyin ta'addanci, zargin da Katar ta musanta tana zargin Saudiyya da raina mata 'yancinta na matsayin kasa mai cikakken iko.