1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Ci gaba da jigilar hatsi duk da barazanar Rasha

August 17, 2023

Jirgin ruwan dakon kaya na farko da ya tashi daga Ukraine bayan cikar wa'adin yarjejeniyar fitar da abinci ta tekun Bahar Al-asuwad na daf da isa gabar ruwan Turkiyya duk da barazanar Rasha.

https://p.dw.com/p/4VIe1
Hoto: Ukraine's Infrastructure Ministry Press Office/AP/picture alliance

Ma'aikatar da ke lura da zirga-zigar jiragen ruwa ta Schulte mai ofishi a birnin Hamburg na kasar Jamus, ta tabbatar da tashin jirgin dakon kayan daga tashar jiragen ruwa ta birnin Odessa da ke Ukraine a ranar Laraba, kuma ta ce tana hasashen zai isa birnin Santabul da Yammacin wannan Alhamis din.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Ukraine ta sha alwashin ci gaba da fitar da abinci ta teku duk kuwa da fatali da Rasha ta yi da sabunta yerjejeniyar da aka cimma a baya karkashin Majalisar Dinikin Duniya da Turkiyya.

To sai shugaba Erdogan na Turkiyya ya ce yana sa ran ganawa da takwaransa Vladimir Putine na Rasha a cikin wannan wata na Agusta, domin samun sahalewarsa kan sabunta yerjejeniyar mai matukar muhimmaci da nufin ceto kasashe mabukata daga fada wa cikin matsalar karancin abinci.