Jiran sakamakon zaɓe a Senegal
February 26, 2007Al´ummar Senegal na cikin jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko ,da ya wakana jiya.
A cewar shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta Mamoudou Moustafa Toure,a jimilce, an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, duk da yan kura kuran da ba su taka karya ba, su ka karya, da a aka samu na da cen.
Ya zuwa yanzu, hukumar, ba ta bayyana sakamakon zaɓen ba, saidai jam´iyar PDS mai riƙe da ragamar mulki, ta nunar da cewa, ta tattara sakamakon mayan biranen ƙasar, kuma babu shakka ɗan takara ta, Abdoullahi Wade, zai yi tazarce tun zagaye na farko.
Sarkin yakin neman zaɓen dan takara Wade, ya ce shugaban zai lashe zaɓen da kashi kimanin 57 bisa 100 na jimilar ƙuri´un da a ka kaɗa.
Magoya bayan jam´iyar PDS, sun share daren jiya, su na taɓi da guda, domin nuna murnar alamun kama hanyar lashe wannan zaɓe.