1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jim Yong Kim ya zama shugaban Bankin Duniya

April 16, 2012

Ɗan takarar ta ƙasar Amurka ya doke abokiyar hammayyarsa kuma ministar kula da harkokin kuɗi a tarrayar Najeriya Ngozi Okonjo Iweala

https://p.dw.com/p/14exE
Jim Yong Kim meets with Brazil’s Economy Minister Guido Mantega, not in picture, in Brasilia, Brazil, Thursday April 5, 2012. U.S. physician Jim Yong Kim is President Barack Obama's nominee for the next World Bank president. (Foto:Eraldo Peres/AP/dapd)
Hoto: dapd

An dai ja daga amma kuma an sha kashi ga ƙoƙarin ƙasashe na masu tasowa na ƙwace kujerar shugabancin bankin duniya da ƙasar Amurka ta share kusan shekaru 70 kanta.

A wani zaɓen da hukumar gudunawar bankin na duniya ta gudanar da yammaciyar litinin a birnin Washington dai ɗan takarar ƙasar Amurka Jim Yong Kim ya doke abokiyar takarar ta sa kuma ministan kudin tarrayar Najeriya Ngozi Okonjo Iweala domin shugabantar cibiyar da ke zaman ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kuɗi na duniya mafi tasiri.

Ana dai kallon zaɓen na Kim ɗan shekaru 52 likita kuma masanin yaƙi da cutar Aids ko Sida a matsayin nasarar ƙarfin ikon Amurka da kawayenta na turai da Japan dake rike da kaso 54 cikin 100 na jarin bankin da kuma suka share sama da shekaru 60 suna cin Karen su babu babbaka a cikin harkokin sa.

An dai ruwaito ita kanta Iwealan na zargin abun da ta kira siyasar ƙarfi maimakon cancantar da ta ce ta mamaye harkokin bankin na lokaci mai tsawo da kuma tai tasiri wajen kaiwa ga zaɓen.

Ngozi Okonjo-Iweala, coordinating minister for economy and finance of Nigeria, speaks during a plenary session at the 42nd annual meeting of the World Economic Forum, WEF, in Davos, Switzerland, Thursday, Jan. 26, 2012. The overarching theme of the meeting, which will take place from Jan. 25 to 29, is "The Great Transformation: Shaping New Models". (AP Photo/Keystone, Jean-Christophe Bott)
Ngozi IwealaHoto: dapd

Sauyin alkibla na da wuya a jagorancin Bankin

To sai dai kuma zaɓen har ila yau na ƙara fitowa fili da jan aikin dake gaban ƙasashen masu tasowar da yanzu haka ke fatan ganin sauyi a cikin harkokin tafiyarwar bankin da kuma suka yi ruwa da tsaki wajen neman fara kaddamar da sauyin nasu tare da zaɓar shugaban da ba na Amurka bane.

Sauyin kuma da a cewar Dr Hussaini Audu dake zaman shugaban ƙungiyar Action Aids mai yaƙi da talauci da kamar wuya a cikin bankin da Amerikar ceke da ikon ƙarshe na faɗa aji.

Siyasar cin zaɓe ko kuma ƙoƙarin sauyi dai babban kalubalen da daga dukkan alamu ke gaban bankin na zaman shawo kan ƙasashe masu tasowar dake iya kallon matakin direktocin bankin 25 a matsayin kokarin maida bankin mallakin Turai da Amurka kaɗai.

Zoellick mai barin gado
Zoellick mai barin gadoHoto: dapd

'Yan makonni kafin zaɓen dai dama an ruwaito 'yayan ƙungiyar BRICS na masu ƙarfin tattalin arziki kuma ke tasowa na barazanar kafa nasu bankin da nufin tabbatar da daidaito a cikin harkokin kuɗi a duniya baki ɗaya.

To sai dai kuma a cewar Dr Bashir Kurfi dake zaman masanin harkokin tattalin arziki a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ƙasashen da ke tasowar basu da ƙarfin sauyin abun da ke faruwa a cikin bankin yanzu.

Majiyoyi dai sun ce akwai yiwuwar saka wa Iweala da mukamin shugabar bankin raya ƙasashen Africa ta ADB. Mukamin kuma da shima kasar ta Amurka ce ke kan gaba da jari mafi yawa a cikin sa.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar