1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jigo a jam'iyyar AfD a Jamus ta nuna goyon bayanta ga Trump

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 7, 2024

Weidel ta bayyana shugaba Joe Biden a matsayin ya gaza, kuma ba shi da wani karsashi da karfin ikon shugabantar Amurka

https://p.dw.com/p/4hzGT
Hoto: Revierfoto/dpa/picture alliance

Daya daga cikin jagororin jam'iyyar AfD mai kyamar baki a Jamus Alice Weidel, ta nuna goyon bayanta ga tsohon shugaban Amurka  Donald Trump a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba mai zuwa, sakamakon alkawarin da ya yi na kin tallafa wa Ukraine da kudi a yakinta da Rasha.

Karin bayani:Joe Biden da Donald Trump na yakin neman zabe a Georgia

Weidel ta nuna kwarin gwiwarta ga Trump kan cewa zai cika alkawarin da ya dauka matukar ya lashe zaben, inda ta bayyana shugaba mai ci Joe Biden a matsayin ya gaza, kuma ba shi da wani karsashi da karfin ikon shugabantar Amurka.

Karin bayani:Biden na zawarcin kuri'un Larabawan kasar

Kamfanin dillancin labaran Jamus DPA ya rawaito cewa Alice Weidel ta yi fatan cewa ina ma dai wasu 'yan takara na dabam ke neman shugabancin Amurka amma ba wadannan biyun ba, inda ta ayyana salon yakin neman zaben Amurka a matsayin ibtila'i.