1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jerin 'yan takara shugabancin Bankin Duniya

March 24, 2012

Bankin Duniya ta bayyana sunayen mutane uku da suka ajje takara maye gurbin Robert Zoellick

https://p.dw.com/p/14R2o
Weltbank Logo

Bankin Duniya ta bayyana sunayen 'yan takara uku da ke bukatar maye gurnin shugaba mai bain gado Robert Zoellich na Amurika.Wannan 'yan takara uku sun ne ministar kudin Nijeriya Ngozi Okonja Iwela, da tsofan ministan kudin Kolumbiya José Antonio Ocampo, da kuma Jim Yong Kim, dan takarar kasar Amurika, wanda ba zato ba tsammani shugaba Barack Obama ya mika sunansa, jim kadan kamin rufe rijistan 'yan takara.

A yayin da yake bayana hujojinsa na dora takara Jim Yong Kim Obama ya ce saboda mutum ne da ya share shekaru da dama, ya na gwagwarmaya domin ci gaban kasashen duniya.

A watan Afrilu mai kamawa za a bayyana wanda ya samu nasara daga 'yan takara ukku.

Bisa al'ada tun lokacin kafa Bankin Duniya dankasar Amurika ke jagorantar ta, saboda haka a wanan karo ma bisa dukan alamu, Amurika za ta yi tazarce, duk kuwa da cewar masana harakokin kudi a duniya, na bayyana karfin takarar Ngozi Okonja Iwela.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala