1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sharhunan jaridun Jamus kan mutuwar Deby

Mohammad Nasiru Awal RGB
April 23, 2021

Labarin mutuwar Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya mamaye sharhuna da labaran da jaridun Jamus suka rubuta kan nahiyarmu ta Afirka a wannan mako.

https://p.dw.com/p/3sTyG
Tschad N'Djamena 2020 | Präsident Idriss Deby Itno
Shugaba Idriss Deby ya mutu yana da shekaru 68Hoto: Blaise Dariustone/DW

Idan muka fara da jaridar Die Tageszeitung cewa tayi, bayan shekaru fiye da 30 a kan mulki, Shugaba Idriss Deby mai shekaru 68, ya rasu a wata fafatawa da 'yan tawaye. Tuni aka nada dansa, Mahamat Idriss Déby Itno mai shekaru 37, shugaban majalisar koli ta soji, da zai jagoranci kasar. Jaridar ta ce gajeriyar sanarwar da shugabannin sojojin Chadi suka bayar a ranar Talata game da rasuwar Idriss Deby, sakamakon ranunuka da ya samu a yaki da 'yan tawayen, Kungiyar FACT a karshen mako, ta kada ilahirin yankin Sahel. Tun a karshen mako rundunar sojin Chadi ke fafatawa da 'yan tawayen a garin Mao mai tazarar kilomita 280 arewa maso gabashin babban birnin kasar wato N'Djamena. A ranar 11 ga watan nan na Afrilu mayakan 'yan tawayen suka bar kasar Libiya suka tsallaka kan iyaka zuwa Chadi, cikin mako guda sun kara dannawa zuwa N'Djamena.

Tschad Mahamat Idriss Déby
Shugaban riko Mahamat Idriss DébyHoto: Kenzo Tribouillard/AFP

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya rasu a wani yanayi da ba a fayyace ba lokacin ziyarar da ya kai wa dakarunsa da ke yakar 'yan tawaye. Wannan ya zo ne kwana guda bayan sake zabansa a wa'adin mulki na shida. Wannan shi ne kanun labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga game da rasuwar shugaban na kasar Chadi. Jaridar ta ce labarin rasuwarsa ya zo da mamaki hatta a kasashen waje. Ta ce shugaban babban aminin kasashen Faransa da Jamus ne a yaki da ta'addanci musamman ma kungiyar G-5 Sahel da aka kafa shekaru bakwai da suka wuce, wadda kuma ta kunshi kasashen Chadi, Mauritaniya, Mali, Burkina Faso da Nijar.  Sai dai a yayin da kasashen yamma ke daukar Deby a matsayin aboki na yaki da ta'addanci, al'ummar Chadi na nuna rashin gamsuwa da gwammatinsa ta kama karya da matsalar talauci da ta yi yawa a kasar mai arzikin man fetur. Faransa da Jamus sun ba da hujjar hadin kai da gwamnatin kama karya ta Chadi da damuwar da ake nunawa na kwararowar 'yan gudun hijira zuwa Turai. Dukkansu kasashen na G-5 na zama asali ko wuaren da 'yan gudun hijira ke ratsawa ciki a kokarin shigowa nahiyar Turai ta barauniyar hanya.

Tschad l Beerdigung von Präsident Idriss Déby Itno | Präsident Macron
Moussa Faki da Macron na FaransaHoto: CHRISTOPHE PETIT TESSON/REUTERS

A karshe sai jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta labarto cewa yawan 'yan gudun hijira daga Afirka zuwa Jamus ya karu. Ta ce duk da cewa Afirka na zama matalauciyar nahiya da ke makwabtaka da nahiyar Turai, kuma wasu yankuna na Afirka na fama da munanan rikice-rikice, amma wani kaso kalilan ne kawo yanzu daga nahiyar suka yi kaura zuwa Jamus. Sai dai yawan 'yan gudun hijirar Afirka a Jamus ya karu sosai a cikin shekaru biyar da suka gabata. Ya zuwa karshen shekarar 2020 yawansu ya kai dubu 123, idan aka kwatanta da dubu 50 a shekarar 2016. Kashi daya bisa hudu yara ne da matasa da suka samu mafaka a Jamus bayan sun tsere daga yake-yake da cin zarafi daga gwamnatocinsu.