1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun Polio a Afirka ya dau hankali a Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 25, 2022

Batutuwan da suka hadar da samar da riga-kafi a Afirka da sake bullar cutar Polio a nahiyar da ma na sojojin hayar Rasha a Afirkan, sun dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/47bVl
Afirka ta Kudu I Cape Town | Afrigen I Allurar Riga-Kafi
Kwararrun kamfanin Afrigen, sun yi nasara samar da riga-kafin corona a Afirka ta KuduHoto: Kristin Palitza/dpa/picture alliance

A sharhinta mai taken "Fata ga Afirka," jaridar Handelsblatt ta ce nahiyar ta dogara matuka kan sayen alluran riga-kafi daga kasashen ketare. Sai dai shugabar kamfanin sarrafa magunguna na Afrigen Petro Terblanche na son kawo sauyi, ta hanyar fara sarrafa alluran riga-kafin da ingancinsu ya yi daidai da na kasashen ketaren a cikin gida. Yanzu haka dai masana kimiyya daga kamfanin na Afrigen sun yi nasarar samar da allurar riga-kafin corona a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu. Kamfanin dai ya yi amfani ne da riga-kafi samfurin Moderna da ake samarwa a Amirka, wajen sarrafa riga-kafin mRNA da tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da kuma wasu kasashe na nahiyar Turai ciki har da Jamus.

Polio a Afirka | Riga-Kafi a Uganda
Sake bullar cutar Polio a Afirka, na haifar da fargabaHoto: Nicholas Kajoba/XinHua/dpa/picture alliance

Polio a Afrika! in ji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cikin sharhinta mai taken: "Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana samun sake bullar Polio a Afirka."  Jaridar ta ce a karon farko bayan tsawon shekaru biyar, an sake samun bullar Polio a Afirka a jikin wani yaro a Lilongwe babban birnin ksar Malawi kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ruwaito. A watan Agustan shekara ta 2020 ne dai, WHO din ta sanar da cewa an kawo karshen Polio a nahiyar Afirka a hukumance. Abin da ya sanya cutar ta zama iya kasashen Pakistan da Afghanistan kadai. A cewar daraktar WHO din a Afirka Matshidiso Moeti in har akwai kwayar cutar Polio a wata nahiya, to tabbas akwai fargabar yiwuwar samunta a sauran nahiyoyin duniyar baki daya. Hukumar dai ta damu matuka ganin cewa yara kanana da dama a kasashe matalauta, ba sa samun riga-kafi yadda ya kamata tun bayan bullar annobar corona.

Mali I Rasha I Sojoji
Ana sukan ayyukan sojojin hayar Rasha a wasu kasashen AfirkaHoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/imago images

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta rubuta nata sharhin ne mai taken: "Ayyukan sojojin hayar Rasha na Wagner a Bangui." Jarida ta ce  Ayyukan sojojin hayar Rasha a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na haifar da cece-kuce. Yayin da Faransa ta bayyana ayyukan da "tsari na cin zarafi" ita kuma Rasha ta bayyana kalaman Faransan da wani "gangami mai tsauri." Sakamakon rikicin da ake fama da shi a Ukraine da Mali ne dai, yayin zaman Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya aka samu cece-kuce tsakanin Faransa da Rashan dangane da takaddamarsu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Kasashen Birtaniya da Amirka da kuma Faransan, sun zargi sojojin hayar Rashan da ke taimakawa gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a yakin da take da 'yan tawaye. Yayin da jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniyar ya bayyana ayyukan sojojin Rashan da "tsari na cin zarafi" da nufin haifar da fargaba da kuma yin iko da wani yanki domin cimma wani buri, takwaransa na Rashan ya bayyana kalaman kasashen da "gangami mai tsauri" a kan "kwararrunsu."

Madagaska I Ambaliyar Ruwa I Mummunar Guguwa I Batsirai
Bala'in guguwa ya haddasa mummunar asara a MadagaskaHoto: Alkis Konstantinidis/REUTERS

Fargabar mummunar guguwa, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Ta ce an tafka mummunar asara a Madagaska, sai dai kasar ba wai bala'in guguwa kawai take fuskanta ba. Jaridar ta ce kasar ta fuskanci guguwar Ana da Batsirai da kuma Emnati. Suna haifar da mummunan asara, inda a makonni biyun da suka gabata tsibirin da ke Tekun Indiya ya fuskanci bala'in guguwa har sau biyu. Tun daga wancan lokaci hanyoyi da dama sun lalace, yayin da ake fama da rashin hasken wutar lantarki a yankuna da dama kana dubban mutane suka rasa matsugunansu ko suka kaura domin su tsira da rayukansu. A cewar Hukumar Kare Afkuwar Bala'o'i ta Madagaskan, kawo yanzu mutane dubu 15 ne bala'in guguwar ya shafa a kasar da ke yankin gabashin Afirka.

Habasha I Masar I Sudan I Madaatsar Ruwa I Hasken Wutar Lantarki
Samar da hasken wutar lantarki daga madatsar ruwan Kogin NiluHoto: Amanuel Sileshi/AFP/Getty Images

Jaridar Süddeutsche Zeitung kuwa ta rubuta nata sharhin ne da taken: "Haske cikin Duhu" Ta ce: Habasha ta fara samar da hasken wutar lantarki daga madatsar ruwa ta Kogin Nilu. Jaridar ta ce, an saka tutocin kasar Habashan a babbar madatsar ruwan. Wannan dai ya zama babban abin tarihi ga Habasha da ma sauran kasashen yankin gabashin Afirka. Shekaru 10 bayan dasa tubalin samar da hasken wutar lantarkin, babbar matasar ruwan ta Afirka ta fara samar da hasken witar lantarkin. Wannan ci-gaban da aka samu dai, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Habashan ke tsaka da yakin basasa.