1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: 20.12.2024

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
December 20, 2024

Ficewar kasashen Kungiyar AES da yakin Sudan da guguwar da ta afka wa Mozambik wadannan sune batutuwan da jaridun Jamus suka mayar da hankali a kai.

https://p.dw.com/p/4oPg9
Hoto: Ubale Musa/DW

Jaridar Zeit Online a sharhinta mai taken: ECOWAS ta sallama wa  Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso, kasashe uku da sojoji suka kifar da gwamnati tare da ayyana fita daga kungiyar ta kasashen Afirka ta yamma a watan Janairun wannan shekara. Jaridar ta ce shugabannin kungiyar habaka tattalin arzikin Kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ko CEDEAO, sun magantu a kan wannan matsala, bayan kusan shekara guda suna ta kokarin samo mafita. Sun yanke shawarar kyale kasashen uku su kama gabansu, wannan babban koma-baya ne. A ranar Lahadin karshen makon da ya gabata kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta amince da jadawalin fitar kasashen ku daga cikinta, inda a yanzu za a tabbatar da ficewar kasashen a hukumance a ranar 29 ga watan Janairun da ke tafe na shekara ta 2025.  Shugaban Hukumar ECOWAS din ko CEDEAO Omar Touray ne ya sanar da hakan, inda ya ce kasashen na Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso za su kammala fita daga cikinta a watan Yuli shekarar ta 2025.

ECOWAS , CEDEAO, AES, Mali, Niger, Burkina Faso, Gipfel, Nigeria , Politik
Hoto: Ubale Musa/DW

Ita kuwa mujallar Faz Net ta rubuta sharhinta ne mai taken: Amfani da biliyoyin kudin zinare wajen daukar nauyin yaki. A Sudan ana fama da mummunan yaki da bai kamata al'ummomin kasa da kasa da Jamus zu zuba ido suna kallo ba, ya kamata a ce tuni sun dauki matakin ladabtarwa ga bangarorin da ke yaki ta hanyar kakaba musu takunkumi kan muhimmin abin da ke samar musu kudi shiga. Jaridar ta ce lamari na kara rincabewa a Sudan, sojojin gwamnati da dakarun 'yan tawaye na RSF na ci gaba da kaddamar da munanan hare-hare. Duka bangarorin biyu sun saba tanade-tanaden dokokin kasa da kasa, wadanda suka wajabta kare rayukan fararen hula. A yanzu haka ba kasar da al'ummarta ke tserewa gidajensu da ke warwatse a cikin kasarsu kamar Sudan a duniya, inda aka kiyasta sun kai sama da mutane miliyan 14 a yanzu ba ya ga wasu miliyan 12 da suka warwatse tun bayan barkewar yaki a watan Afrilun 2023. A yanzu haka kuma sama da rabin al'ummar kasar na fama da matsananciyar yunwa, kiyasi ya nunar da cewa sama da mutane miliyan 25 wannan matsala ta shafa.

APTOPIX Mayotte Cyclone Chido
Hoto: Adrienne Surprenant/AP/picture alliance

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta rubuta sharhinta ne mai taken: Rashin samun taimako bayan mahaukaciyar guguwa a unguwar talakawa ta Mayotte, har yanzu ko gawarwakin wadanda suka mutu yayin ibtila'in ba a kai ga ganowa ba. Mozambik ma ta fada cikin bala'i, bayan mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da "Chido" ta afku a yankin Mayotte a Tsibirin Comoros da ke karkashin ikon Faransa a gabar ruwan Tekun Indiya, a yanzu ta isa Mozambik. A nan ma ta yi mummunar barna, kamar yadda rahotanni suka nuna. Rahotannin farko da suka fito daga hukumar kare afkuwar bala'o'i ta Mozambik a ranar Talatar da ta gabata sun nunar da cewa, kimanin mutane 34 suka halaka yayin da sama da gidaje 20 suka rushe. Faifen bidiyo na farko da ya fito daga Mozambik din ma, ya nuna yadda mahaukaciyar guguwar ta lalata gidaje a gundumar Cabo Delgado da ke yankin arewacin kasar. A wannan yanki ne dai mayaka masu ikirarin jihadi suka kwashe tsawon shekaru suna kai hare-hare a kan sojoji, abin da ya janyo dubban mutane uska kauracewa gidajensu tare da zama a sansanonin 'yan gudun hijira na cikin gida.

Formel 1 I Kämpfen um die Weltmeisterschaft I Max Verstappen  und Lewis Hamilton
Hoto: Xavi Bonilla/PanoramiC/imago images

Ba mu karkare da jaridar Neue Zürcher Zeitung da ta rubuta sharhinta mai taken, gasar tseren motoci na shirin komawa Afirka. Ruwanda ta nemi daukar nauyin babbar gasar ta Grand Prix, yayin da Afirka ta Kudu ta Marokko ba su da kyakkyawan fata. A ta bakin Alexander Wurz da ke zaman shugaban kungiyar direbobin tseren motoci kana tsohon dan wasan tseren motocin na Ostiriya, tuni shirye-shiryen gasar ta Ruwanda ta dau harami bayan da ya kwashe tsawon lokaci yana san ya idanu a Kigalin. A makon da ya gabata Shugaba Paul Kagame na Ruwandan, ya mika takardar neman daukar nauyin gasar ta Formula 1 da kasarsa ke son daukar nauyi. Wannan mataki dai zai tabbatar da lakanin da ake wa kasar na "kasar dubban tuddai." Ko da yake har ynazu Ruwandan kyakkyawan fata kawai take da shi, amma akwai yiwuwar gudanar da babbar gasar da ake kira da Grand Prix a Kigali.