1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan na son farfado da tattalin arzikin Afirka

Ramatu Garba Baba
August 27, 2022

Japan ta ware kimanin dala biliyan 30 don tallafa wa Afirka farfadowa daga ta'asar da annobar corona da yakin Rasha da Ukraine suka yi wa tattalin arzikin nahiyar.

https://p.dw.com/p/4G8QL
Tunesien, Tunis | Japan - Afrika Gipfel
Hoto: Fethi Belaid/POOL/AFP/Getty Images

Shugabanin kasashen Afirka da Japan da kungiyoyin kasa da kasa sun fara taron shekara na habaka kawancen ci-gaban Afirka.Taron na gudana ne a birnin Tunis na kasar Tunisiya.Tuni Japan ta yi alkawarin tallafa wa Tunisiya da dala miliyan dari don rage radadin annobar corona ga tattalin arzikin kasar baya ga tallafin na dala biliyan talatin ga sauran kasashen Afirka. Matsaloli na tsaro da ta'asar annobar corona dama yakin Rasha da Ukraine na daga cikin batutuwan da mahalarta taron za su tattauna da zummar samar da mafita.

Shugaban Japan Fumio Kishida bai samu damar halartar taron na bana ba a sakamakon kamuwa da ya yi da cutar corona. Gwannatin Japan ce ta samar da TICAD a shekarar 1993 kafin ya zama na hadin gwiwa, bayan da Majalisar Dinkin Duniya da babban bankin duniya dama Kungiyar tarayyar Afirka suka hada kai, wajen lalubo hanyoyin da za a ciyar da nahiyar Afirka gaba da kuma magance matsalolin da suka hana mata ruwa gudu.