Japan ta gabatar da daftarin kudurin jan kunnen Koriya Ta Arewa
July 8, 2006Talla
Duk da adawa da Rasha da kuma China ke nunawa, Japan ta gabatar da wani daftarin kuduri ga kwamitin sulhun MDD wanda ya tanadi sanyawa KTA takunkumin karya tattalin arziki, saboda gwaje gwajen makamai masu linzami da ta yi baya bayan nan. Kasashen Amirka, Birtaniya da kuma Faransa na goyon bayan daftarin kudurin amma kamar yadda jami´an diplomasiya suka nunar, an dage kada kuri´a a kai har zuwa ranar litinin. Mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amirka Christopher Hill yayi kira ga gamaiyar kasa da kasa musamman ma China da su dauki matsayi daya akan wannan rikici. Yanzu haka dai Hill na tattaunawa da mai shiga tsakani na KTK, Chun Young-Woo a birnin Seoul akan sabon halin da ake ciki.