1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da zaben 'yan majalisa a Japan

July 10, 2022

Firaministan Japan Fumio Kishida wanda zai fi amfana da sakamakon zaben, ya ce kisan gillar da aka yi wa tsohon firaministan kasar Shinzo Abe ba zai dakatar da cika sharudan da dimukuradiyya ta yi tanadi ba.

https://p.dw.com/p/4DuhB
Japans Regierungschef Fumio Kishida
Hoto: Kyodo News/AP/picture alliance

An bude runfunan zaben 'yan majalisa a fadin kasar Japan a wannan Lahadi. Ana sa ran zaben zai kara wa jam'iyyar tsohon Firaminista Abe goyon baya, bayan kisan gillar da aka yi masa a wajen yakin neman zabe na jam'iyyarsa ta LDP don nema wa 'yan takara a jam'iyyarsa tagomashi.

Idan har jam'iyyar ta LDP ta yi nasara kamar yadda ake hasashe, Kishida zai samu damar ci gaba da zama firaministan Japan har nan da shekaru uku ba tare da an sake komawa zabe ba.