1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan na bankwana da Shinzo Abe

Binta Aliyu Zurmi
July 12, 2022

Cikin kuka da alhini al'umma a Japan na bankwana da tsaohon Firaministan kasar Shinzo Abe.

https://p.dw.com/p/4DzGy
Japan | Beerdigung Shinzo Abe
Hoto: Yoshitaka Nishi/Yomiuri Shimbun/AP Photo/picture alliance

Da safiyar wannan Talatar ce 'yan uwa da abokai na kusa da tsohon Firaministan kasar Japan Shinzo Abe ke ban kwana da gawarsa a yayin gudanar da jana'izarsa a wani wurin ibada.

Iyalansa ne kadai da kuma wasu mutane kalilan aka amincewa su halarci jana'izar, sai dai al'ummar kasar sun yi dandazo a kan layi a wani gurin ibadar inda suke kuka suna nuna alhinin rabuwa da tsohon Firaministan wanda ya rasu sakamakon mummunan raunin da ya samu bayan harbinsa da wani dan bindiga ya yi a karshen makon da ya gabata.

Ana ci gaba da tsare dan bindigan da ya yi sanadin rayuwar Shinzo Abe wanda tun da farko ya dauki alhakin kisan ba tare da yin nadama ba.