1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janye tallafi kan 'yan gudun hijira

Gazali Abdou TasawaJune 4, 2016

Shugaban Turkiyya ya yi barazanar kyale Turai da matsalar 'yan gudun hijira idan Jamus da Turai ba su canza matsayinsu ba a game da batun zargin Turkawa da aikata kisan kare dangi.

https://p.dw.com/p/1J0fr
Türkei Ankara Präsident Recep Tayyip Erdogan
Hoto: Getty Images/AFP/A. Altan

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi barazanar kyale Turai da matsalar 'yan gudun hijira matsawar Jamus ba ta canza matsayinta ba a game da batun zargin da ta ke yi wa Turkawa da aikata kisan kare dangi kan Armeniyawa a lokacin yaki duniya na farko.

Shugaba Erdogan ya bayyana haka ne a lokacin wani jawabi da ya gabatar a wannan Asabar a gaban tarin jami'an gwamantinsa inda ya ce kasarsa ba za ta taba amincewa da wannan zargi ba har abada. A ranar Alhamis da ta gabata ce dai majalisar dokokin Jamus ta kada kuri'ar amincewa da kisan Armeniyawa da ake zargin Turkawa da aikata a lokacin yakin duniya na farko a matsayin kisan kare dangi, zargin da Turkiyyar ke musantawa.