Sojan Nijar sun yi sabon shugaba
April 3, 2023Duk da rashin karin bayani daga fadar shugaban kasa game da dalilan sauke tsohon shugaban hafsan sojojin kasar ba Janar Salfou Modi daga mukaminsa kwanaki biyu bayan kara masa galar girma, ba zato ba tsammahani ne shugaban kasar Nijar ya maye gurbinsa da Janar Abdou Sidikou Issa wanda ya taba rike mukaman shugabancin sojoji da dama da suka hada da shugaban hafsan sojojin kasa na kasar.
Karin Bayani: Yunkurin samar da zaman lafiya mai dorewa
'Yan Nijar na yi wa matakin sauke shugaban hafsan sojojin kasar da maye gurbinsa da sabon shugaba kwanaki biyu bayan kara masa gala fassara, Moussa Aksar dan jarida bai binciken kwakwaf kana kwararre a fannin harkokin tsaro ya bayyana cewa matakin sauke tsohon shugaban hafsan sojan Nijar na zuwa ne a yayin da ake ganin yana dab da ritaya, kuma shugaban kasa kadai ya san dalilan da suka sa ya sauke shi daga mukamin."
Karin Bayani: Makarkashiyar ta'addanci a yankin Sahel
Masu sharhi na ganin cewa ko baya ga batun tsaro a iyakokin kasar, rikicin ta'addanci a yankin Diffa da Tillabery na daga cikin muhimman kalubalen da ke gaban sabon shugaban hafsan sojojin kasar da ya kamata ya mayar da hankali kansu.
A makobciyar kasar Nijar Burkina Faso ma shugaban mulkin rikon kwaryar soji na kasar, ya gudanar da garambawul a rundunar sojojin kasar, kuma jama'a sun zura ido su ga tasirin da hakan za ´ya yi wajen shawo kann matsalar ta'addanci musmamana a yankin magngamar iyaka uku na Nijar Mali da Burkina Faso.