Janar Babacar Gaye ya fara jagorantar sanya idanu a rikicin Siriya
July 26, 2012Talla
Janar ɗin wanda ɗan asalin kasar Senegal ne zai jagoranci tawagar soji ɗari da hamsin domin gudanar da aiyyukan sanya idanu na tsawon kwanaki talatin bayan da kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tsawaita wa'adin aikin dakarun da ke sayan idanu kan rikicin na Siriya.
Cigaba da aikin na dakarun na Majalisar Ɗinkin Duniya dai na zuwa ne daidai lokacin da ake cigaba da gwabza faɗa tsakanin dakarun gwamnatin ƙasar da masu rajin kawo sauyi.
Masu aiko da rahotanni dai na cewar dakarun ɓangarorin biyu na ƙara yawan mutanensu a garin Aleppo da kuma Damuscas, fadar gwamnatin ƙasar a wani yunƙuri na karɓe iko da yankunan.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu