1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jan Egeland ya maida martani ga haramcin da gwamnatin Sudan tayi masa na ziyartar Darfur

April 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2u

Mataimakin sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da bada agaji, Jan Egelend, ya maida martani, da haramcin da hukumomin Sudan su ka yi masa, na kai ziyarar gani da ido a yankin Darfur.

Idan ba a manta ba ranar, litinin da ta wuce, gwamnatin Khartum ,ta ƙi baiwa Sakataren, izinin gudanar da rangadi a wanan yanki , da ke fama da yaƙe yaƙe.

A cikin martanin da ya maida, Jan Egeland, ya bayyana matukar takaici ,ga wannan mataki da hukumomin Sudan su ka ɗauka.