1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus:Za ta ci gaba da taimaka wa Afirka

Abdourahamane Hassane
May 3, 2018

Ministan harkokin waje na Jamus Heiko Maas ya ce Jamus ba za ta manta ba da nahiyar Afirka, ya bayyana haka ne a lokacin wata ziyara da ya kai a kasar Habasha.

https://p.dw.com/p/2x7DI
 Heiko Maas ministan harkokin waje na Jamus
Heiko Maas ministan harkokin waje na JamusHoto: DW/G. Tedla

Heiko Maas ya ce ko da shi ke hankalinsu ya dauku a game da abin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, amma gwamnatin Jamus ba ta manta ba, da Afirka ba. Minista na harkokin waje na Jamus Heiko Maas ya yi alkawarin cewar Jamus za ta  ci gaba da hulda da nahiyar Afirka ta fuskar taimakata a kan sha'anin tsaro da tattalin arziki. Wannan shi ne rangadi na farko da ministan yake yi a wasu kasashen Afirka wadanda suka hada da Habasha da kuma Tanzaniya makwannin shida da ya fara aiki.