1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hulda tsaanin Jamus da Girka

Abdourahamane Hassane
January 11, 2019

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za su taimaka wa Girka a game da batun matsalar bakin.

https://p.dw.com/p/3BO0t
Griechenland, Athen: Staatsbesuch Angela Merkel und Prokopis Pavlopoulos
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Shugaban Kasar Girka Prokopis Pavlopoulos Hoto: Reuters/A. Konstantinidis

Angela Merkel ta bayyana haka ne a birnin Athens na Girkar inda ta soma ziyarar aiki bayan ta gana da shugaban kasar Prokopis Pavlopoulos. Sannan kuma shugabar gwamnatin ta ce Jamus ta amince da daukar nauyin kisan kare dangi da gwamnatin 'yan Nazi ta aiwatar a Girkar a tsakanin shekara ta 1941 zuwa 1944. Tsananin bashin da ya yi wa Girka katutu ya sa an sake zafafa muhawarar da aka dade ana yi, na ganin cewar Jamus din ta biya kudaden diya ga Girka a sakamakon cin zarafin bil Adama da gwamnatin 'yan Nazi ta yi a kasar a lokacin yakin duniya na biyu.