1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus za ta sa ido kan iyakokinta

October 16, 2023

Wannan wani mataki ne da Jamus ta bijiro da shi don dakile safarar miyagun abubuwa da ta bil'adama ta barauniyar hanya

https://p.dw.com/p/4Xaut
Grenze Tschechien-Deutschland
Hoto: Ondrej Hajek/CTK/picture alliance/dpa

Nan ba da jimawa ba gwamnatin Jamus za ta sanar wa kungiyar tarayyar Turai shirinta na tsaurara bincike a kan iyakokinta da kasashen Poland da Jamhuriyar Czech da kuma Switzerland, domin dakile safara da kuma shige da ficen da ake yi ta barauniyar hanya.

Ministar harkokin cikin gidan Jamus Nancy Faeser ce ta sanar da hakan yau Litinin, inda ta ce kamar yadda 'yan sanda ke gudanar da sintiri a kan iyakar Jamus da Austria tun a shekarar 2015, to haka za rinka yi a kan iyakokinta da wadannan kasashe da ke makotaka da ita.