1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkawalin cika sharadin da NATO ta kafa Jamus na kan hanya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 1, 2019

Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta bayyana cewa kasar zata ware kaso daya daya da rabi na tattalin arzikinta ga sojoji kan nan zuwa shekarar 2024 a wani mataki na biyayya ga sharadin da NATO ta gindaya.

https://p.dw.com/p/3N6wO
Verteidigungsministerin besucht Einsatzführungskommando
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Settnik

Da ta ke magana karon farko a gaban manema labarai bayan ganawarta da babban sakataren zartawar kungiyar NATO a kasar Bejiyam. Annegret Kramp-Karrenbauer ministar tsaron ta Jamus ta ce Jamus na daga cikin abukanin huldar kut da kut na kungiyar tsaro ta NATO kana kuma za ta kara jadadda hakan a gaba.

Ya zuwa yanzu dai kasashe mambobin kungiyar NATO da suka cika wannan sharadi na sanya kaso biyu cikin dari na kasafin tattalin arzikinsu ba su wuce shida ba kawai, a yayin da kasashen kamar Faransa da Jamus da ke a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai suka kasa cimma wannan matsayi, batun da kuma shugaba Donald Trump na Amirka ya sha suka yana mai bayyana cewa kasa yin haka da Jamus ta yi kasawa ce.