1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus tana ci gaba da taimakon Ukraine

Suleiman Babayo ATB
April 20, 2022

Gwamnatin Jamus ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da taimakon Ukraine da makamai na zamani, bayan kutsen da Rasha ta kaddamar kan kasar.

https://p.dw.com/p/4A96V
Außenministerin Baerbock im Baltikum | Lettland Außenminister Rinkevics
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Kasar Jamus ta bayyana shirin taimakon kasar Ukraine kan harkokin soja na matsakaici da dogon lokaci. Ministar harkokin wajen kasar ta Jamus Annalena Baerbock ta bayyana haka a wannan Laraba lokacin ganawa da takwaranta na Latviya, Edgars Rinkevics a birnin Riga fadar gwamnatin kasar ta Latviya.

Ministar harkokin wajen ta Jamus ta ce kasarta za ta ci gaba da tura kayan yakin ga Ukraine, kuma za a sabunta makaman kasar ta Ukraine da na zamani.

Haka na faruwa kokacin da Rasha take kara azama a kutsen da ta kaddamar a kan kasar ta Ukraine. Dubban sojojin kasar ta Rasha suna ci gaba da kutsawa yankin Danbas na gabashin Ukraine da ya bayyana ballewa, kuma yake dauke da 'yan aware masu goyon bayan Rasha.