1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jordan na fama da matsalar durkushewar tattali

Zainab Mohammed Abubakar
June 21, 2018

Shugabar gwamnati Angela Merkel ta sanar da wannan tallafin, daura da yarjejeniyar kasashen biyu da ya kawo ga adadin tallafin dala miliyan 442, a wannan shekara ta 2018.

https://p.dw.com/p/301NO
Deutschland Berlin - König Abdullah von Jordanien trifft Angela Merkel
Hoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

   

 Merkel ta yi alkawarin ba wa Jordan karin rancen dala miliyan 100, kasar da gangamin adawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati ya tilasta fraiminista yin murabus a farkon wannan wata na Juni.

A jawabinta ga daliban jami'ar Jamus da ke Jordan a kusa da birnin Amman, Merkel ta ce har yanzu Jamus ce kasar da ke maraba da 'yan gudun hijira da da baki 'yan kasashen waje;

" Ina ganin bai kamata ku ji tsoro ba. Dole ne wasu su fadi abunda bai kamata ba dangane da batun 'yan gudun hijira, sai dai hakan zai iya faruwa a ko'ina. Amma a dunkule zan iya alfaharin cewar, babu kasa kamar Jamus idan aka zo batun kare lafiyar 'yan gudun hijira, duk da cewar a wasu lokuta sun fuskanci zargi da ma kai musu hari, har da kisan gilla ga 'yan mata 'yan gudun hijira". 

Ziyarar ta yini biyu ta Merkel a yankin Gabas ta Tsakiya, na zuwa ne a daidai lokacin da rigingimu kan batun karbar 'yan gudun hijira ke kara ta'azzara a siyasar cikin gida na Jamus.