1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalliya ba ta biyan kudin sabulu kan dokokin corona a Jamus

December 10, 2020

Kimanin mutane kusan dubu ashirin ne ke kamuwa da cutar Corona a ko wace rana a Tarayyar Jamus, in ji cibiyar Robert Koch.

https://p.dw.com/p/3mWr2
Berlin I Kabinettssitzung I Angela Merkel
Hoto: Markus Schreiber/AP/picture alliance

Alkaluman masu kamuwa da Corona a Jamus na cigaba da daukar hankullan mahukuntan kasar, bayan da suka bayyana cewa dokokin hana yaduwar cutar da ake bi a halin yanzu basa biyan bukata.

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Markel, ta bukaci da a karfafa dokokin hana yaduwar annobar nan da kamin a fara bukukuwan Kirsimati gadan-gadan, wadanda suka hada da tsawaita hutun 'yan makaranta da kuma rufe wuraren kasuwanci.

Haka zalika cibiyar Robert Koch ta ce alkaluman masu kamuwa da cutar a ko wace rana kan kai kimani 20,000, kamar yadda shugaban cibiyar Lother Wieler ya jinjina lamarin.

Lother Wieler ya ce yanayin yadda ake samun masu kamuwa da cutar ya ta'azzara musamman a 'yan makwannin nan, kawo yanzu lambar na cigaba hauhawa.