1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Tantance masu neman mafaka a wata kasa

Abdullahi Tanko Bala
June 21, 2024

Gwamnatin Jamus za ta ci gaba da yin nazarin matakan wasu kasashe na tantance masu neman mafakar siyasa inda ta ke fatan samar da nata tsarin na daban.

https://p.dw.com/p/4hLK5
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Markus Schreiber/AP Photo/picture alliance

Daga cikin matakan da gwamnatin ke nazari sun hada da yarjejeniyar tantance masu neman mafaka da Italiya ta yi da Albania sannan Burtaniya itama ta kulla irin wannan yarjejeniya da Rwanda domin tantance masu neman mafaka.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya tabbatar wa da gwamnonin jihohi cewa gwamnatin za ta ci gaba da nazarin tantance bukatun masu neman mafakar a wata kasa ta daban.

Ya ce zai gabatar da shawarwarinsa a taro na gaba da za a yi tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi a watan Disamba.