1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta tsawaita dokar kullen corona

January 5, 2021

Yayin da ake ci gaba da aikin rigakafin cutar corona a Jamus, hukumomin kasar sun sake tsawaita wa'adin kullen corona a fadin kasar har zuwa karshen watan Janairu.

https://p.dw.com/p/3nXu0
Berlin I Angela Merkel verkündet Verlängerung des Lockdowns
Hoto: Michel Kappeler/REUTERS

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da wasu shugabannin jihohi 16, sun amince da sabbin matakan yaki da cutar corona a kasar, abin da ya sanya su kara tsawaita dokar kulle zuwa karshen wannan wata na Janairu.

Matakan sun hada da tsaurara tafiye-tafiye a kewayen akalla kilomita 15 ga mazauna yankunan da annobar ke da kamari a cikin su.

Wani matakin shi ne sake tsaurara hani a kan taron jama'a, inda haduwa ba za ta wuce ta mutum guda tsakanin mazauna mabambanta gidaje ba.

Dama dai a yanzu mutum biyar-biyar daga gidaje biyu na iya haduwa a lokaci guda.