1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta taka rawa wajen musayar fursunoni da Rasha

Abdullahi Tanko Bala
August 2, 2024

Gwamnatin Jamus ta taka muhimmiyar rawa wahen musayar fursunoni tsakanin Rasha da kasashen yamma inda Mosco ta sako fursunoni 16 domin musaya da yan Rasha takwas da ake tsare da su a kasashen yamma

https://p.dw.com/p/4j1hF
Musayar fursunoni da Rasha - Filin jirgin saman Köln Bonn
Musayar fursunoni da Rasha - Filin jirgin saman Köln BonnHoto: Marvin Ibo Güngör/Bundesregierung/Getty Images

Babban jigo a musayar fursunoni da ya hada kasashe da dama shi ne Vadim Krasikov, dan Rasha da aka yanke wa hukuncin zaman kaso bisa samunsa da kisan wani tsohon dan gwagwarmayar Chechenya a Berlin a shekarar 2019.

 

Rasha ta gabatar da tayin musayar fursunonin ga Amurka a 2022 domin sako mata Krasikov wanda ke zaman daurin rai da rai a Jamus. Sai dai saboda Krasikov ba dan asalin Amurka ba ne, Jami'an Amurka basu bai wa tayin wani muhimmanci ba.

 

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya fada a kwanan nan a cikin wani shirin talabijin na Tucker Carlson cewa a shirye shirye ya ke domin musayar fursunonin da Krasikov.

 

Shawarar sakin Krasikov dai batu ne na siyasa mai sarkakiya ga Jamus, bisa la'akari da girman laifin kisan wanda ya auku da rana tsaka a wani dandali a kusa da majalisar dokoki da kuma ofishin shugaban gwamnatin Jamus a Berlin