Jamus ta shirya bai wa Siriya tallafin kudade
December 12, 2024Gwamnatin kasar Jamus ta ce za ta samar da karin kudaden da yawan su zai kai euro miliyan takwas, kwatankwacin dala miliyan takwas din da dubu 400 domin taimaka wa Siriya ta fuskar agaji.
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, ta ce lokaci ne da Siriya ke hangen sabon fata na samun daidaituwa.
Baerbock ta kuma ce za atsara shirin mayar da 'yan Siryia kasarsu da kawaye na nahiyar Turai da ma Majalisar Dinkin Duniya.
Sannan kuma ta yi kira ga kasashen Isra'ila da Turkiyya da kada su kawo cikas ga shirin kafa sabuwar gwamnati a Siriya bayan kawo karshen ta hambararren Shugaba Bashar al-Assad.
A halin yanzu dai, Firaminista mai rikon kwaryar gwamnatin Siriya, Mohammed al-Bashir ya yi kira ga 'yan kasar da suka tsere zuwa wasu yankuna na duniya da su koma gida, yana mai cewa kasar ta gano daraja da karfinta.