1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sabuwar shekara a Jamus da zabe

Suleiman Babayo ZUD
December 31, 2024

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci hadin kai tsakanin 'yan kasar, a cikin sakon da ya gabatar yayin da ake shiga sabuwar shekara ta 2025, inda kasar za ta gudanar da zaben kasa baki daya a farkon shekarar.

https://p.dw.com/p/4oi0I
Olaf Scholz | Shugaban gwamnatin Jamus
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf ScholzHoto: Soeren Stache/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya bukaci hadin kai tsakanin 'yan kasar yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara ta 2025. A jawabinsa na shiga sabuwar shekara duk da matsalolin da yake fuskanta da kuma matsin lamba da ya janyo shirya zabe da wuri, Scholz ya jaddada tasirin aiki tare da karfafa wa juna.

Karin Bayani: Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus?

Sannan ya yi godiya wa jami'an tsaro da ma'aikatan agaji na kokrin da suke yi musamman lokacin harin da aka fuskanta a kasuwar Kirsimeti na garin Magdeburg inda mutane biyar suka halaka kana wasu fiye da 200 suka jikata. Shugaban gwamnatin na Jamus, Olaf Scholz ya karfafa gwiwa wa mutane kan kada kuri'a da wuri a zaben kasa da zai wakana ranar 23 ga watan Febrairu mai zuwa. An kira zabenbayan rushewar gwamnatin hadaka tsakanin jam'iyyu uku.