1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta shiga farautar wasu 'yan ta'adda 14

October 25, 2016

'Yan sanda a Jamus sun kaddamar a wannan Talata da wani aikin bincike a yankuna biyar na kasar domin farautar wasu Rashawa 'yan asalin kasar Tchetcheniya su 14 da ake zargi da alaka da Kungiyar IS

https://p.dw.com/p/2RgKG
Anti-Terror-Einsätze der Polizei in Thüringen
Hoto: picture-alliance/dpa/B.Schackow

'Yan sanda a nan Jamus sun kaddamar a wannan Talata da wani aikin bincike a yankuna biyar na kasar domin farautar wasu Rashawa 'yan asalin kasar Tchetcheniya su 14  masu neman takardar izinin zaman kasa a Jamus da ake zargi da samar da kudaden gudanarwa ga kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma kasancewa masu alaka da Kungiyar IS. 

Jami'an 'yan sandan sun kai samame a gidaje 12 a biranen Thuringen na jihar Saxony ta Gabashin kasar da a birnin Hambourg na Arewaci da a yankin Bavariya na Kudancin kasar. Ana zargin mutanen 14 dukkaninsu 'yan shekaru 21 zuwa 31 da suka hada da mata uku da kasancewa masu alaka da wani matashi mai shekaru 28 dan asalin kasar Tchetcheniya wanda a shekara ta 2015 ya yi yinkurin zuwa kasar Siriya domin shiga Kungiyar IS. 

Sai dai a cikin wata sanarwa da hukumomin 'yan sandar birnin na Thuringen suka fitar sun ce har kawo yanzu dai sakamakon binciken nasu bai gano wani hadari na yiwuwar fuskantar hari ba, amma dai suna ci gaba da gudanar da binciken nasu.