1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jamus ta shawarci Isra'ila a kan zaman lafiya a Zirin Gaza

September 6, 2024

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da aikinta na fadada matsugunai a yankin gabar yammacin kogin Jordan, yayin wata ziyara da take yi a Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/4kMgc
Annalena Baerbock da ministan wajen Isra'ila Israel Katz
Annalena Baerbock da ministan wajen Isra'ila Israel KatzHoto: GIL COHEN-MAGEN/AFP

Ziyarar ta Baerbock a yankin dai na da nasaba ne da kokarini da ake yi na ganin an cimma tsagaita wuta a yakin Isra'ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza.

Babbar bukatar ita ce ta ganin an sako 'yan Isra'ila da ke hannun kungiyar Hamas da kuma kara agajin jinkai a Zirin Gaza da yaki ya daidaita.

Gabanin isar babbar jami'ar diflomasiyyar Jamus din a birnin Tel Aviv, Baerbock ta ziyarci kasashen Saudiyya da kuma Jordan.

Watanni 11 da fara yaki a tsakanin Isra'ila da Hamas, cikin wannan makon gwamnatin Amurka ta ce akwai alamun samun nasarar cimma tsagaita wuta da ake buri.